Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zamanin Ƙanƙara

Gabatarwa

Zamani Ƙanƙara, wanda ake kira Ice Age ko Glacial Age a Turance, zamani ne da aka yi a baya wadda ya zama mafi tsananin sanyi a duk zamuna har ta kai ga ruwan teku ya sandare ya zama dusar ƙanƙara wadda kuma ya wanzu na tsawon dubun nan shekaru.

Shekaru kusan dubu talatin da biyu da ashrin da ɗaya (30,000 B.C. - 2021 A.D.) ko kuma dubu talatin da shida/bakwai da ashirin da ɗaya (35,000/36,000 B.C. - 2021 A.D.) da suka shuɗe, an yi wannan zamani da ya samar da kafar da ta zama labar da mutanen Nahiyar Asiya (Asian Continent) daga yankin Saberia (Siberia) suka ƙetara zuwa Nahiyar Amurka ta Arewa (North American Continent) ta gefen Alaska wadda wannan guri yanzu ya zama makekiyar ƙasa Tarayyar Jahohin Amurka.


Taswirar yankunan duniya da za a iya ganin Amurka da Asiya a kai.
Hoto: Nation Online

Ma’anar Zamanin Ƙanƙara

Ray (Babu shekara), ya bayyana Zamanin Ƙanƙara a matsayin: “Wani zamani na yawaitar yaɗuwar dusar ƙanƙara”. Sai kuma Britannica Encyclopaedia (2020), da suka ce Zamanin Ƙanƙara shi ne: “Dukkan zamanin sauyin yanayin da kakkaurar dusar ƙanƙara ta lulluɓe makeken yankin dandagaryar ƙasa. Tare da cewa, wannan manya-manyan dusar ƙanƙara suna iya wanzuwa tsawon miliyoyin shekaru, su kuma sauya sifar dandagaryar ƙasar nahiya guda a bayyane”.

Faruwar Zamanin Ƙanƙara

Ko sau nawa wannan zamani na ƙanƙara ya afku a duniya? Haƙiƙa wannan zamani ya afku sau adadin da kiyaye shi ke da wahala, amma masana da suka haɗa da A & E Television Network (2015), sun ce: “Tabbas kuma a taƙaice an samu afkuwar muhimman Zamunan Ƙanƙara guda biyar da suka afku a tarihin duniya a cikin shekaru miliyan ɗaya (1,000,000,000) da suka shuɗe.”

Asali

Jami’ar Illinois (2021) da ke Tarrayar Jahohin Amurka ta bayyana cewa: “Louis Agassiz ne mutumin farko da ya fara kardadon cewa duniya ta taɓa afkawa cikin Zamanin Ƙanƙara. Ya yi tayin wannan kardado nasa ga wata ƙungiya mai suna Helvetic Society a cikin shekarar 1837 kuma abin ya ɗau hankali sosai.”

Tun wancan zamani (1837), masana suke ta gasa alƙaluma da takardu wajen ganin sun ƙalailaice wannan kardado nasa wanda kuma ya zuwa wannan lokaci hujjojin afkuwar hakan suke ta bayyana a tarihance da kuma kimiyyar tarihi (archeology) da sauran hanyoyin zamani da masana ke bi wajen tabbatar da afkuwar wani abu a zamunan da suka shuɗe.

Manazarta

A & E Television Network, (2015). Ice Age. An ciro a 2021, daga https://www.history.com/topics/pre-history/ice-age

Britannica Encyclopaedia (2020). Ice age. Encyclopedia Britannica. https://www.britannica.com/science/ice-age-geology

Jami’ar Illinois (2021). The Life and Work of Louis Agassiz. An ciro a 2021, daga https://publish.illinois.edu/louisagassiz/ice-ages/

Ray L.L. (Babu shekara). The Great Ice Age. U.S. Department of Interior/U.S. Geological Survey. An ciro a 2021, daga https://pubs.usgs.gov/gip/ice_age/ice_age.pdf


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub